Ba Italy Ba Russia 2018

Zakarun kwallon duniya karo hudu, Italiya ta gaza kai wa gasar Cin Kofin Duniya karon farko tun cikin 1958 bayan an lallasa ta a wani wasan fitar da gwani da Sweden.

Hakan na nufin kungiyar kwallon kafar Italiya ta Azzurri ba za ta halarci gasar ba a karo na biyu kenan cikin tarihi bayan ta ki taka rawa a farkon bude gasar Cin Kwallon Kafa na Duniya a 1930.

Dungurar wani da kwallon dan wasan tsakiyar Sweden Jakob Johansson ta yi kuma ta fada raga a karawar farko ta zama sanadin fitar da Italiya duk da wasan da suka yi zagaye na biyu a filin San Siro na birnin Milan inda aka tashi canjaras ba ci.

Sweden ta yi amfani da damar da ta samu kuma duk da rike kwallon da masu masaukin baki suka yi har kashi 75%, amma dai sun gaza yin wani gamon katar – Italiya ta samu babbar dama ta hannun Stephan El Shaarawy amma golan Sweden Robin Olsen ya sa hannu ya ture.

Sakamakon ya ba wa kungiyar Sweden ta Jan Andersson damar kai wa ga Gasar Kofin Duniya karon farko tun bayan shekara ta 2006.

Mfeseer Chiv
About Mfeseer Chiv 1855 Articles
Remember Me When Am Gone. Contact For Event Coverage, Music/Video Publication.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.