‘Direbobi sun kona bankin Diamond a Lagos’

Rahotanni daga birnin Ikko na jihar Lagos na cewa wani dan sanda da ke gadin bankin Diamond a unguwar Apapa, ya harbi wani direban motar haya.

A take dai wanda aka harba din ya mutu.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa hakan ya sa rayukan mutanen da ke wajen musamman sauran direbobi suka baci suka yi kan ‘yan sandan da ke gadin bankin, inda su kuma suka ruga cikin bankin don neman mafaka.

Wani ganau ya ce ganin hakan ya sa sauran direbobin suka cinnawa bankin wuta.

“Tuni aka turo ‘yan sandan kwantar da tarzoma wajen, har ma kuma sun kama wasu mutane sun yi gaba da su,” in ji mutumin wanda ba ya so a ambaci sunansa.

Wajen da ala’marin ya faru dai wuri ne na hada-hadar jama’a sosai, ana kuma yawan yin dakon mai a manyan motoci.

Zuwa yanzu dai ba a san irin barnar da wutar da aka cinnawa bankin ta jawo ba, amma zuwa jimawa za mu kawo muku karin bayani.

A Najeriya dai ana yawan samun irin wadannan rigingimu inda wasu lokutan jami’an tsaro ke kashe mutane ba bisa ka’ida ba su kuma ‘yan kasa suke daukar doka a hannunsu.

Mfeseer Chiv
About Mfeseer Chiv 1855 Articles
Remember Me When Am Gone. Contact For Event Coverage, Music/Video Publication.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.