Connect with us
Yan bindiga sun sace 'yan makaranta shida a Legas

Hausa News

Yan bindiga sun sace ‘yan makaranta shida a Legas

Yan bindiga sun sace ‘yan makaranta shida a Legas

Yan bindiga sun sace ‘yan makaranta shida a Legas

Yan sanda a Legas sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace ‘yan makaranta guda shida.

‘Yan bindigan sun kai hari ne a makarantar Igbonla Model School ranar Alhamis, inda suka tafi da ‘yan makaranta 10.

Amma rahotanni sun ce sun saki hudu daga cikin yaran, bayan da suka binciki asalin iyayensu.

‘Yan sanda sun ce ‘yan bindigar sun sami shiga makarantar ta cikin wani daji da ke gefen makarantar ne, inda suka yanka wayar da ta zagaye makarantar kana suka shiga ciki.

Suka kara da cewa a yanzu jami’an tsaro sun dukufa domin binciken inda ‘yan bindigar suka tafi da yaran.

An taba sace dalibai shida a watan Oktoban da ya gabata a wannan makaranta.

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya.

Click to comment

Leave a Reply, Comment Below

Editors

Fiverr Profile

More in Hausa News